An samu man fetur a Bauchi – NNPC

1503

Example HTML page

An samu man fetur a Bauchi – NNPC
(BBC )
Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya bayyana cewa an samu danyen man fetur a Barambu da ke kauyen Alkaleri na jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.

Mukaddashin mai magana da yawun hukumar Samson Makoji ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a.

A ranar 2 ga watan Fabrairun 2019 ne dai Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaddamar da hakar danyen man fetur a wata rijiya da ke Kogin Kolmani II.

An bayyana cewa an haka rijiyar ne da babban inji mai suna ”IKENGA RIG 101” inda aka haka kusan kafa 13,701, kuma an samu mai da iskar gas a matakai daban-daban yayin hakar da aka yi.

Kamfanin ya yi bayanin cewa a ranar 10 ga watan Octoba da misalin 6:02 na yammaci, an haka rami cikin daya daga cikin rijiyoyin inda aka ga sinadarin hydro carbon ya fara fitowa, kusan da misalin karfe 9:20 na dare kenan.

Ana sa ran kamfanin na NNPC zai kara hako wasu rijiyoyin domin kara samun wasu sinadaren na hydro carbon a tafkin Gongola.
Za mu tsage gaskiya a ayyukan NNPC – Kyari
Abubuwan da ba ku sani ba kan sabon shugaban NNPC
Zan sayar da NNPC ko za a kashe ni —Atiku
Samun mai da iskar gas mai yawa a tafkin Gongola zai taimaka matuka wajen samun masu zuba hannayen jari da kuma samar da ayyukan yi domin samun riba da kuma gwamnatin kasar ta samu kudaden shiga.
Man fetur na daya daga cikin abubuwan da Najeriya ta dogara da shi domin samun kudaden shiga.
Ko kasafin kudin kasar ma ana gina shi ne kan hasashen samun kudi daga gangunan danyen man fetur din da za a sayar biyo bayan kudaden haraji.
Haka zalika kasar na daya daga cikin mambobin kungiyar OPEC wacce kungiya ce ta kasashe masu arzikin man fetur.

Sai dai duk da arzikin danyen man fetur din da kasar take da shi, matatun man kasar ba su tace mai isashe da kasar ke samarwa sai an fitar da shi ketare domin a tace a dawo da shi cikin kasar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here