An Kaddamar Da Fara Ginin Makarantar Kashe Gobara A Katsina

865

Example HTML page

An Kaddamar Da Fara Ginin Makarantar Kashe Gobara A Katsina

A yau talata 15/10/2019 aka kaddamar da mikawa shugaban hukumar aikin kashe Gobara ta kasa da filin da za’a gina makarantar domin horar da ma’aikatan aikin kwana kwana masu kashe gobara.

An dai kaddamar da bayar da filing ne agarin Kankia na jihar katsina

Sanata mai wakiltar shiyyar Daura a jihar katsina sanata Ahmad Babba Kaita ne ya nemo wannan makaranta a matakin gwamnatin tarayya.

Makarantar dai ta daukacin arewa maso yamma ce baki daya

An bada filin gina makarantar ga shugaban hukumar kashe gobara ta kasa (FEDERAL FIRE SERVICE) Dakta Ibrahim Liman, Shugaban hukumar ya bada tabbacin cewa nan da zuwa watan daya na shekara mai zuwa 2020 aikin gina makarantar zai ci gaba.

“maigirma shugaban kasa M Muhammadu Buhari ya bada izinin fidda kudin gina makarantar.

Samun wannan makaranta ya biyo bayan kudiri da sanata mai wakiltar shiyyar Daura jihar Katsina Senata Ahmad Babba Kaita ya gabatar gaban zauren majalisar Dattawan Nijeriya na bukatar gina wannan makaranta.

Hakika Kudirin sanata ya karbu gashi har za’a ci gaba da fara gudanar da bada horo karkashin wannan makaranta a mazaunin wuccin gadi a garin Kankia, kafin kammala gina mazaunin makarantar na dindin wanda yake bisa hanyar kano garin Kukar Kwaida cikin karamar hukumar Kankiya.

Taron kaddamar da bada filin ya samu halartar iyaye kasa hakimin kankiya da hakimin Rimaye , kantoman rikon karamar hukumar Kankiya Honarabul Musa Maikudi Kankiya,Kantoman ƙaramar hukumar Kusada Honarabul Sama’ila Kusada, da Shuwagabannin Jama’iyya na shiyya dana ƙananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Kankiya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here