Sanata Ndume ya jinjina wa Sojojin Najeriya

902

Example HTML page

Sanata Ndume ya jinjina wa Sojojin Najeriya

(Tambari)

Shugaban Kwamitin Sojoji a Majalisar Dattawa Sanata Muhammad Ali Ndume ya yabawa rundunar Sojan Najeriya saboda ci gaba da samar da zaman lafiya musamman a garin Gwoza na jihar Borno.

Ndume a cikin sakon fatan alheri yayin gabatar da kambun shaidar lambobin yabo ga wasu dakarun sojojin rundunar Operation Lafiya Dole a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, ya tuna cewa, ‘yan shekaru da suka gabata idan aka ce wa mutum ya ze Gwoza, za ka yi tunanin wancan mutumin baya son ka saboda a lokacin babu tsaro amma da taimakon Sojojin Najeriya, yau an kubutar da Gwoza daga ‘yan Boko Haram.

A cewarsa, “A madadin mutanen Gwoza muna amfani da wannan dama domin godewa Sojojin Najeriya kuma za mu ci gaba da yi muku addu’ar samun nasara a yaki da kuke yi.”

Ya yi kira ga Shugaban Hukumar bunkasa Yankin Arewa Maso Gabas, Alhaji Goni da ya kasance tare da taimakawa wajen sake gina garuruwan Kirawa, Asgaciya, Ngishe, Madube da Bita domin a cewar sa yankunan na da bukatar kulawar hukumar.

Shima a nashi jawabin, Babban Hafshin Hafsoshin Sojan Kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce ya zama dole ya karrama rundunar bisa kwazo da kwarewa tare da sadaukarwa da suke nunawa a ci gaba da wanzar da zaman lafiya da suke yi a Arewa maso Gabas.

Ya bukace su da su kasance masu biyayya da maida hankali wajen sauke nauyin da aka ba daura musu, ya kuba tabbatar musu cewa jin dadin su da na iyalansu dake gida shine babban abin da ya sa a gaba.

Buratai ya mika godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari, Gwamnatin Tarayya da Majalisar tarayya ta kasa saboda ci gaba da goyon baya da suke basu ta kowani fanni.

Shi ma a nashi jawabi, Shugaban Kwamitin Sojoji a Majalisar Wakilai Honorabul Abulrazak Namdas ya jinjina wa dakarun Sojojin Najeriya tare da shugabancin TY Buratai.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron sun hada da babban bako na musamman mai girma Ministan Tsaro wanda Daraktan Sojoji Mista Musa Sunday Attah ya wakilta, da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa Cif Seth Crowther, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan Sojoji Sanata Ali Ndume, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sojoji Hon. Abdurazaq Namdas. Saura sun hada da Sarakuna, da ‘yan siyasa, jami’an Soji, mafarauta da sauran su.

5 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here